zazzau emirate assured kadchma of total supports for health care KANUN LABARI: MASARAUTAR ZAZZAU TA TABBATAR DA CIKAKKEN GOYON ...
KANUN LABARI: MASARAUTAR ZAZZAU TA TABBATAR DA CIKAKKEN GOYON BAYANTA GA KADCHMA DOMIN INGANTA KIYAYE LAFIYA
Masarautar Zazzau ta tabbatar wa Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Kiwon Lafiya ta Jihar Kaduna, wato KADCHMA, cikakken goyon baya da haÉin kai domin ganin an cimma nasarar ĘoĘarin Gwamnatin Jihar Kaduna na inganta harkokin kiwon lafiya a faÉin jihar.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tuntuba da dabarun wayar da kai da ya haÉa shi da Hakimai 31 na Masarautar Zazzau da manyan jami’an masarautar, tare da jami’an KADCHMA da abokan hulÉar ci gaba.
Sarkin Zazzau ya bayyana cewa kiwon lafiya na daga cikin muhimman abubuwan da Éan Adam ke buĘata a rayuwarsa, inda ya ce KADCHMA ta ziyarci fadar masarautar sau da dama domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin shiga tsarin da kuma fa’idodin da ke tattare da shi.
Mai Martaba Sarkin ya umarci dukkan Hakimai 31 da sauran masu hali a cikin masarautar da su bayar da cikakken goyon baya tare da Ęarfafa mutane da su yi rajista cikin shirin, domin rage yawan kashe kuÉaÉen aljihu da mutane ke yi wajen neman magani.
Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya bayyana cewa mutane da iyalansu kan kashe makudan kuÉaÉe a duk wata wajen kula da lafiyarsu, amma kafa KADCHMA ya zo da tsarin da zai sauĘaĘa wa al’umma samun kiwon lafiya ta hanyar biyan kuÉin rajista na shekara-shekara.
Mai Martaba Sarkin ya kuma nuna goyon bayansa ga shirin ta hanyar yin rajistar mutane kusan 100 daga cikin ma’aikatan masarautar. Haka kuma, KADCHMA ta bai wa Masarautar Zazzau damar yin rajistar mutane 1,000 kyauta daga cikin al’ummomin da ke ĘarĘashin Hakimai 31 na masarautar.
Tun da farko, Darakta-Janar na KADCHMA, Alhaji Abubakar Hassan Dujiman Jama’a, ya yaba da irin gudunmawar da Mai Martaba Sarkin Zazzau ke bayarwa wajen ganin shirin ya yi nasara, yana mai cewa ba za a iya Ęididdige muhimmancin ĘoĘarinsa ba.
Alhaji Abubakar Hassan ya ce a ko da yaushe Ęofar fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau a buÉe take ga KADCHMA, yana mai cewa irin wannan haÉin kai zai taimaka wajen kai shirin ga jama’a a matakin Ęananan hukumomi da Ęauyuka.
Ya bayyana cewa KADCHMA wani tsari ne da ake tara gudunmawar kuÉi domin biyan kuÉin ayyukan kiwon lafiya ga mazauna Jihar Kaduna. Ya Ęara da cewa Gwamna Malam Uba Sani ya sha nanata kudirinsa na inganta harkokin kiwon lafiya, yayin da shirin KADCHMA ke biyan kuÉin ayyukan kiwon lafiya da ake bai wa waÉanda suka yi rajista a cibiyoyin kiwon lafiyar da suka zaÉa.
A jawabansu daban-daban, wakilan abokan hulÉar ci gaba da suka halarci taron sun bayyana irin gudunmawar da suke bayarwa a fannoni daban-daban, musamman a harkokin rigakafi, kula da iyali da sauran shirye-shiryen kiwon lafiya.
Ęaya daga cikin abokan hulÉar ci gaban, Alhaji Garba Shehu, ya shaida wa wakilinmu cewa tawagarsu za ta yi aiki kafada da kafada da Masarautar Zazzau domin cimma manufofin shirin da kuma tabbatar da cewa wayar da kan jama’a ta isa ga al’ummomi a faÉin masarautar.
Taron ya kuma gudana ne da Ęaddamar da Kwamitin Kiwon Lafiya na Masarautar Zazzau da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi, inda ya buĘaci kwamitin da ya tabbatar da gaggauta Éaukar matakai da kuma ingantaccen haÉin gwiwar ayyukan kiwon lafiya a cikin masarautar.
A Ęarshen taron, jami’an KADCHMA sun kai ziyara kasuwar Sabon Garin Zaria, inda aka buÉe sabon ofishin KADCHMA domin sauĘaĘa wa jama’a samun damar yin rajista da kuma Ęara wayar da kan al’umma game da tsarin.
Wakilinmu, Mikail Ibrahim Fagachi, ya ruwaito.

No comments