Mikail Ibrahim Fagachi An bayyana rabon tallafin kuɗi da sauran kayayyakin tallafa wa iyayen marayu a dukkan gundumomi goma sha...
Mikail Ibrahim Fagachi
An bayyana rabon tallafin kuɗi da sauran kayayyakin tallafa wa iyayen marayu a dukkan gundumomi goma sha uku na ƙaramar hukumar Zariya a matsayin wani yunƙuri na rage raɗaɗin halin matsin tattalin arziki da kuma tallafa wa marasa galihu a cikin al'umma.
Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Mazabar Zariya a ƙarƙashin jam'iyyar NDC a zaɓen shekarar 2027, Alhaji Hamisu Idris Maiganda, ne ya bayyana haka yayin shirin rabon tallafin da aka gudanar a Zariya.
Alhaji Hamisu Idris Maiganda ya ce ya daɗe yana gudanar da irin wannan shiri a matsayin wani ɓangare na ƙudurinsa na taimaka wa marasa galihu, musamman marayun da suka rasa masu kula da su. Ya bayyana cewa halin ƙuncin rayuwa da ake ciki a yanzu na buƙatar masu hannu da shuni, ƙungiyoyi masu zaman kansu, gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa su ƙara ƙaimi wajen taimaka wa mabukata.
Ya ce bayar da jari ga iyayen marayu zai ba su damar dogaro da kai ta hanyar gudanar da ƙananan sana'o'i maimakon zama mabarata. Haka kuma ya buƙaci al'umma su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda tare da zaɓen shugabanni nagari da za su iya magance matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
A jawabansu daban-daban, Sakataren jam'iyyar NDC na Jihar Kaduna, Malam Balarabe Ayuba, da shugabar mata ta yankin Arewa maso Yamma ta jam'iyyar, Hajiya Fatima, sun bayyana wannan shiri da Honarabul Hamisu Idris Maiganda ya gudanar a matsayin hujja ta nagartar shugabancinsa da kuma damuwarsa kan jin daɗin al'umma. Sun ce shirin na daga cikin manufofin jam'iyyar NDC, tare da kira ga al'ummar Mazabar Tarayya ta Zariya da su ba shi goyon baya a zaɓen shekara ta 2027.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun shaida wa Nagarta Radio farin cikinsu bisa wannan tagomashi, inda suka ce tallafin zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da kula da iyalansu.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da kuɗaɗen tallafi da suka kai har naira dubu dari uku, babura, injinan ɗinki da sauran kayan tallafawa.
Manyan baƙi da suka haɗa da 'yan siyasa, shugabannin addinai, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki sun halarci taron.
Daga Zariya, ni ne Mikail Ibrahim Fagachi, mai rahoto na Nagarta Radio Kaduna.

No comments