Mikail Ibrahim Fagachi. Al'ummomin da ke amfani da hanyar Zariya–Soba–Pambegua–Saminaka mai tsawon kusan kilomita saba'i...
Mikail Ibrahim Fagachi.
Al'ummomin da ke amfani da hanyar Zariya–Soba–Pambegua–Saminaka mai tsawon kusan kilomita saba'in da biyar na ci gaba da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran hanyar saboda irin mawuyacin halin da suke fuskanta. Hanyar dai tana haɗa ƙananan hukumomi huɗu zuwa biyar, kuma tana da muhimmanci wajen zirga-zirga da bunƙasa tattalin arziƙi a yankin.
Wasu daga cikin mazauna yankunan sun shaida wa wakilin Nagarta Radio cewa an gina hanyar ne kimanin shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar da suka gabata, amma ba a taɓa gudanar da cikakken aikin gyara ba tun daga lokacin. Sun ce galibin mazauna yankin manoma ne da ke samar da dimbin amfanin gona iri-iri, sai dai lalacewar hanyar na hana su sauƙin kai amfanin gonarsu kasuwanni.
Al'ummomin sun kuma bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata sun yi ƙoƙarin fara aikin gyaran hanyar a lokuta daban-daban, amma daga bisani aka yi watsi da aikin bayan an fara shi, lamarin da ya sa hanyar ta ci gaba da lalacewa.
Haka kuma, wasu daga cikin mazauna yankin sun tunatar da cewa kimanin shekaru biyu da suka gabata, Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Arewa, Barista Ibrahim Khalid Soba, tare da mambobin Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ayyuka, sun ziyarci hanyar tare da yin alƙawarin ganin an gyara ta. Sai dai sun ce har zuwa yanzu babu wani gagarumin ci gaba da aka samu.
A yayin da aka tattauna da direbobin ababen hawa da fasinjojin da ke amfani da hanyar, sun bayyana cewa lalacewar hanyar na jawo yawaitar lalacewar motocinsu, inda bayan kusan kowace tafiya sai sun kai mota gareji domin gyara. Haka kuma, sun ce hakan ya sa kuɗin sufuri suka ninka saboda tsadar kula da motocin.
Al'ummomin yankunan sun yi kira ga dukkan zaɓaɓɓun shugabanninsu da suka haɗa da 'yan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, 'yan Majalisar Wakilai, Sanata Barista Ibrahim Khalid Soba da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da su gaggauta ɗaukar matakin gyaran hanyar domin rage wahalhalun da jama'a ke fuskanta tare da bunƙasa harkokin noma da kasuwanci a yankunan.
Daga Mikail Ibrahim Fagachi a Zaria.

No comments