Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Tsohon Ɗan Takarar kujerar Gwamnan Kaduna a Jam'iyar ADC, Mainan Zazzau, Ya Fice Daga Jam'iyyar

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Farfesa Muhammad Sani Bello, Mainan Z...


Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Farfesa Muhammad Sani Bello, Mainan Zazzau, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

A cikin wata takardar  murabus da ya Sanyawa  hannu mai ɗauke da kwanan watan 21 ga Yuli, 2026, wadda ya aika wa Shugaban Jam'iyyar ADC na Gundumar Dogarawa da ke Zariya, Farfesa Bello ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar nan take.

Farfesa Sani Bello Ya gode wa shugabanni da mambobin jam'iyyar bisa kyakkyawar alaƙa da  haɗin kai da goyon bayan da suka ba shi a tsawon lokacin da yake cikinta.

Sai dai bai bayyana dalilin ficewarsa daga jam'iyyar ba. 

Ya kuma yi wa jam'iyyar da mambobinta fatan alheri a harkokinsu na gaba, tare da roƙon a amince da matakinsa cikin girmamawa.


No comments