Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma mai taimakon al’umma, Malam Magaji Umar Dan Aljanna, ya taya daukacin al’ummar Mus...
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma mai taimakon al’umma, Malam Magaji Umar Dan Aljanna, ya taya daukacin al’ummar Musulmin duniya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Malam Magaji Umar Dan Aljanna ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen tunawa da kyawawan dabi’u da halayen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, tare da kokarin koyi da su a rayuwarsu ta yau da kullum.
Ya ce rayuwa bisa koyarwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam za ta taimaka wajen inganta zaman lafiya, hadin kai, tausayi da kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma.
Malam Magaji Dan Aljanna ya kuma bukaci al’umma da su yi amfani da wuraren tarukan Maulidi wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali.

No comments