Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

ALUMMAR TURAWA KARAMAR HUKUMAR SOBA SUN KOKA KAN YADDA AIKIN GINA SABUWAR HANYAN TURAWA KURUNGUFI ZUWA DINYA KE TAFIYAN HAWAINIYA

ALUMMOMIN TURAWA A KARAMAR HUKUMAR SOBA SUN KOKA KAN YADDA AIKIN GINA SABUWAR HANYAN TURAWA KURUNGUFI ZUWA DINYA KE TAFIYAN HADI...

ALUMMOMIN TURAWA A KARAMAR HUKUMAR SOBA SUN KOKA KAN YADDA AIKIN GINA SABUWAR HANYAN TURAWA KURUNGUFI ZUWA DINYA KE TAFIYAN HADI DA ROKON MAIGIRMA GWABNAR JIHAR KADUNA KAN HANYAN 

Al'ummar yankin Turawa da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da ita a Ƙaramar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna sun bayyana damuwarsu kan jinkirin kammala aikin gina titin da ya haɗa Turawa, Kurungufi, Daha zuwa Dinya, tare da zargin cewa ana samun ƙarancin inganci a wasu sassan aikin.

Shugaban Ƙungiyar Raya Al'ummar Turawa (Turawa Development Association), Alhaji Abdullahi Muntari Turawa, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala rangadin duba yadda aikin ke gudana tare da tawagar 'yan jarida. Ya fara da yabawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa amincewa da aiwatar da aikin titin, yana mai cewa idan aka kammala shi zai sauƙaƙa zirga-zirga, ya bunƙasa kasuwanci da harkokin tattalin arziki, musamman a ranakun kasuwa ga al'ummomin da ke amfana da titin.

Alhaji Abdullahi Muntari ya ce duk da muhimmancin aikin, al'umma na nuna damuwa kan yadda aikin ke tafiya a hankali da kuma abin da suka ce ana iya gani da ido na ƙarancin inganci a wasu wurare. Ya bayyana cewa sun sha tattaunawa da kamfanin da ke aikin domin bayyana damuwarsu, duk da cewa sun san ba ƙwararru ba ne a fannin aikin gina tituna.

Ya buƙaci al'ummar yankin su ci gaba da kasancewa masu haƙuri tare da ba da cikakken haɗin kai, sannan ya roƙi Gwamnatin Jihar Kaduna da Hukumar Ƙaramar Hukumar Soba da su riƙa sanya ido akai-akai domin tabbatar da cewa ana gudanar da aikin bisa ƙa'ida kuma an kammala shi cikin lokaci.

A nasu jawaban daban-daban, Sarkin  Turawa, Alh Dahiru  Umar da Sarkin Daha da Dinya sun nuna godiyarsu ga Gwamnatin Jihar Kaduna bisa bayar da kwangilar aikin. Sun kuma yabawa kamfanin da ke aikin saboda ci gaba da gudanar da shi duk da Æ™alubalen da ake fuskanta, tare da kira ga al'umma da su kasance masu haÆ™uri, zaman lafiya da bin doka a kowane lokaci.

 Har'ila yau mun tattauna da wasu direbobi, fasinjoji da sauran mazauna yankin, inda suka nuna farin cikinsu da aikin titin, amma suka buÆ™aci a hanzarta kammala shi tare da tabbatar da inganci domin ya É—ore kuma ya amfani al'umma yadda ya kamata.

Da yake zantawa da wakilin Compass Times a wurin aikin, Wakilin É—an kwangilar, Engr  Kachalla ya bayyana cewa ana gudanar da aikin ne bisa Æ™a'idoji da sharuÉ—É—an da ke cikin kwangilar. Ya ce wasu daga cikin korafe-korafen da ake yi na samo asali ne daga rashin cikakken fahimtar yadda ake gudanar da aikin gina tituna. Ya gode wa al'ummar yankin bisa haÉ—in kan da suke bayarwa, ya roÆ™e su da su Æ™ara haÆ™uri, tare da tabbatar musu cewa nan ba da jimawa ba za a kammala aikin. Haka kuma ya roÆ™i Gwamnatin Jihar Kaduna da ta yi la'akari da inganta titin da ya haÉ—a Turawa zuwa Soba

No comments