Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, ya kai ziyarar tarihi zuwa Makarantar Nuri-Tilawah International School,...
Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, ya kai ziyarar tarihi zuwa Makarantar Nuri-Tilawah International School, Zariya, inda ya jaddada aniyyarsa na tallafawa ci gaban karatun Al-Qur’ani da inganta tarbiyyar Addinin Musulunci tare da yabawa kokarin da makarantar ke yi.
A jawabinsa yayin ziyarar, Daraktan Makarantar, Sheikh Nuraddin Umar Tahir, ya bayyana gamsuwa da farin ciki kan wannan ziyara, yana mai cewa masarautar Katsinan Gusau ta yi fice wajen ilimi, shugabanci na gari da hidimar addini tun zamanin jihadin Mujaddadi Shehu Usman Bin Fodiyo.
Sheikh Tahir ya kuma mika ta’aziyya kan rasuwar tsohon Sarkin Katsinan Gusau, wanda shi ne mahaifin Sarkin yanzu, tare da taya shi murna bisa hawa karagar mulki a matsayin Sarki na 16 na Katsinan Gusau.
Ya kuma gode wa shuwagabannin kwamitin amintattu na makarantar ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Amb. Ahmad Nuhu Bamalli da Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura da kuma sauran dattawan da suke marawa makarantar baya
Daraktan ya yi addu’a don samun zaman lafiya da cigaba a jihohin Zamfara da Sakkwato, tare da kira ga al’umma su ci gaba da daraja karatun Qur’ani da tarbiyya.
Da yake maida jawabi, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau Abdulkadir Ibrahim Bello, ya yi godiya kan kyakkyawar tarbar da aka yi masa, tare da yabawa jajircewar makarantar wajen inganta karatun Qur’ani da gyaran halaye.
Ya ja hankalin al'umma kan muhimmancin Qur’ani wajen gina nutsuwa, hazaka da gyaran zamantakewa, sannan ya yi alkawarin ci gaba da haɗin gwiwa da makarantar domin dorewar nasararta.
> “Za mu ci gaba da tallafawa cibiyoyin Qur’ani irin su Nuri-Tilawah, domin wannan aiki ne na alheri ga makomar 'ya’yanmu da ci gaban al’umma,” in ji Sarki.
Yayin taron kuma wasu daga cikin daliban makarantar sun karanto wasu daga cikin ayoyin Al-Qur’ani mai girma
Makarantar Nuri-Tilawah International School, Zaria, tuni ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin da suke ba da gudunmawa mai ma’ana wajen ilimin addinin Musulunci a Najeriya. A cikin ɗan gajeren lokaci, makarantar ta sami karɓuwa saboda tsarin koyarwa mai inganci, tarbiyya, da kuma jajircewar malamai wajen gina matasa masu kishi da ilimi.
Makarantar ta kuma samar da ɗaruruwan ɗaliban da suka kammala haddar Al-Qur’ani cikin nutsewa da fahimtar tafsir. Wasu daga cikinsu sun ci gasa a matakai daban-daban na musabaqar Qur’ani a jiha da kasa, lamarin da ya ƙara wa makarantar kima da suna.
Nuri-Tilawah International School ba ta takaita ga haddar Qur’ani kaɗai ba; tana koyar da sauran darussan addinin musulunci tare da dabarun koyar da Qur’ani cikin fasaha da tsaftataccen lafazi.
Makarantar ta sami goyon bayan sarakuna da manyan malamai kamar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar da Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli da Sauran manyan sarakuna daga jihohin Arewaci da Kudancin Najeriya. tare da tallafin malaman jami’a da dattawa.
Daya daga cikin manyan nasarorin makarantar shi ne mayar da hankali kan gyaran halayya, ladabi da tsaftar hali, wanda ke bayyana a rayuwar ɗalibai. Nuri-Tilawah ta yi fice wajen haifar da matasan da suka san darajar tarbiyya a wajajen makaranta da wajen ta.
Makarantar na da malamai ƙwararru, masu ilimi da gogewa, waɗanda ke amfani da sabbin hanyoyin koyarwa da na’ura mai kwakwalwa wajen koya Qur’ani da addini. Wannan ya ba makarantar damar tunkarar zamani ba tare da rasa asali ba.


No comments