Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Kungiyar 'yan Jarida reshen Jihar Kaduna Ta Karrama Ambasada Magaji Dan Aljannah da Lambar Yabo ta Ayyukan Jin Kai

Kungiyar 'yan Jaridu reshen Jihar Kaduna Ta Karrama Ambasada Magaji Dan Aljannah da Lambar Yabo ta Ayyukan Jin Kai Kungiyar ...

Kungiyar 'yan Jaridu reshen Jihar Kaduna Ta Karrama Ambasada Magaji Dan Aljannah da Lambar Yabo ta Ayyukan Jin Kai

Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa,  reshen Jihar Kaduna, ta karrama Ambasada Malam Magaji Dan Aljannah da Lambar Yabo ta Ayyukan Jin Kai na Musamman, bisa gudummawar da yake bayarwa wajen tallafa wa marasa galihu da kuma jin dadin al’umma.

An gabatar da lambar yabon ne a yayin bikin Makon 'yan Jarida  na shekarar 2025 da aka gudanar a Kaduna, wanda ya  tattaro ‘yan jarida, 'yan siyasa Jami'an Gwamnati da masu tsara manufofi da sauran masu ruwa da tsaki domin nazari kan rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen ci gaban kasa.

Bikin Makon 'yan  Jarida ya kunshi gabatar da lambobin yabo da kuma jawabin bita na jama’a da aka gudanar a Arewa House, Kaduna.

A cewar Kungiyar 'yan Jaridan reshen Jihar Kaduna, karrama Ambasada Magaji Dan Aljannah ya yi daidai da al’adar kungiyar na yaba wa mutane da suka yi fice wajen hidimtawa al’umma ba tare da son kai ba, tare da tasiri mai kyau ga zamantakewar jama’a.

Kungiyar ta bayyana cewa gudummawar jin kai da Ambasadan ke bayarwa, musamman wajen tallafa wa mabukata da shirye-shiryen raya al’umma, sun sa ya samu girmamawa da yabo a fadin Jihar Kaduna da ma wajen ta.

An gudanar da taron Makon 'yan Jaridan na 2025 ne karkashin taken: “Kafofin Watsa Labarai da Tsarin Zaman Lafiyar Kaduna: Karfafa Tattaunawa, Tsaro da Ci Gaba a Arewa.”

Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, General Martins Luther Agwai (Rtd), ne ya jagoranci taron, yayin da Mai na Shugaban kasa shawara a harkoki  Tsaron Kasa, Mallam Nuhu Ribadu, ya gabatar da babban jawabin bita.

Shugaban Ƙungiyar NUJ na Kasa, Kwamared Alhassan Yahya, ne ya mika lambobin yabo ga wadanda aka karrama.

Da yake jawabi bayan karbar lambar yabon, Ambasada Malam Magaji Dan Aljannah ya gode wa NUJ reshen Jihar Kaduna bisa wannan karramawa, inda ya ce hakan zai kara masa kwarin gwiwar ci gaba da ayyukan jin kai.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da kuma masu rike da mukaman jagoranci da su nuna tausayi da jinkai ga talakawa, musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.

A cewarsa, “Wannan lokaci ne da masu galihu ya kamata su tausaya wa talakawa tare da mika musu hannu. Idan muka tallafa wa marasa karfi, muna taimakawa wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban al’umma.”

Ambasada Dan Aljannah ya sha alwashin kara fadada ayyukan jin kai domin shafar rayuwar jama’a da dama, tare da yabawa NUJ kan rawar da take takawa wajen inganta gaskiya, adalci da kyawawan dabi’u ta hanyar aikin jarida na gari.

A karshe, NUJ reshen Jihar Kaduna ta sake jaddada kudirinta na amfani da dandalin Makon 'yan Jaridan wajen karfafa tattaunawa, karrama nagarta da kuma karfafa hadin kai domin gina al’umma mai zaman lafiya da wadata.

No comments