Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Lalong ya bukaci tsoffin ɗalibai su cigaba da taka rawa wajen ƙarfafa haɗin kai da cigaban ƙasa

Tsohon gwamnan Jihar Filato kuma Sanata Simon Bako Lalong ya jaddada muhimmancin rawar da ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai ke takawa w...


Tsohon gwamnan Jihar Filato kuma Sanata Simon Bako Lalong ya jaddada muhimmancin rawar da ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai ke takawa wajen bunƙasa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban ɗorewa a Najeriya.

Lalong ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na 18 na Ƙungiyar Tsoffin Ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello da aka gudanar a babban harabar jami’ar dake Samaru, Zariya.

Ya ce irin waɗannan ƙungiyoyi suna zama gadar haɗin kai tsakanin mutane daga kabilu, al’adu, da fannoni daban-daban, suna taimakawa wajen fahimtar juna da haɗa kan al’umma.

Lalong ya jaddada cewa ilimi musamman a jami’o’in da suka yi fice kamar Jami’ar Ahmadu Bello — shi ne ginshiƙin haɗin kan ƙasa mai bambancin al’adu kamar Najeriya. Ya kuma shawarci matasa da tsoffin ɗalibai su wuce sha’anin takardar karatu kaɗai, su bayar da gudunmawa ta ainihi ga ci gaban ƙasa.

> “Ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai suna haɗa mutane daga kabilu da fannoni daban-daban. Ta wannan hanya ne za mu iya rushe bambance-bambance, mu haɓaka tattaunawa, mu ƙarfafa haɗin kan ƙasa,” in ji shi.



Sanata Lalong, wanda shi ne bako mai jawabi, ya bayyana cewa ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai na taka muhimmiyar rawa wajen raya ɗabi’un ɗan ƙasa nagari, haɓaka jagoranci, da tabbatar da zaman lafiya a ƙasa mai ƙabilu da yawa kamar Najeriya.

Ya yi kira ga gwamnati, hukumomin ilimi, da ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai da su ƙarfafa haɗin gwiwa domin shawo kan matsaloli irin su rashin tsaro, rashin aikin yi.


Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, wanda shi ne ya jagoranci taron ya ce gwamnatin tarayya ta samu ci gaba sosai wajen yaki da rashin tsaro a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa an bullo da sabbin dabaru da manufofi don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa tare da ƙarfafa matasa ta hanyar samar da ayyukan yi da rage talauci.

> “Tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne; dole al’umma su bayar da tasu gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji shi.



Badaru ya yabawa Jami’ar Ahmadu Bello bisa gudunmawar da take bayarwa wajen haɓaka bincike, kirkire-kirkire, da horar da shugabanni, yana mai cewa jami’ar na daga cikin manyan cibiyoyin ilimi da ke jagorantar ci gaban ƙasa.


Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya yaba wa jami’ar Ahmadu Bello bisa kasancewarta cibiyar ƙwarewa da haɗin kai.
Ya ce jami’ar ta dade tana zama wuri da ke haɗa ’yan Najeriya daga sassa daban-daban, tana kuma taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba.

> “Jami’ar Ahmadu Bello na daga cikin manyan cibiyoyin haɗin kan ƙasa. Tsoffin ɗalibanta na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya,” in ji shi.



Tun farko a nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Tsoffin Ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello ta Duniya, Malam Adamu Mamman Kontagora, ya gode wa manyan baki da mahalarta taron bisa goyon baya.
Ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da tallafawa jami’ar wajen cimma manufofinta na ilimi da ci gaban al’umma.

Ya ce ƙungiyar za ta ƙara mayar da hankali wajen shirin ba matasa horo da tallafi, da inganta bincike da ƙwarewa a fannoni daban-daban.

No comments