Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Hukumar Kashe Gobara Ta Yaba wa Magaji Dan Aljanna Kan Gina Mata Katafaren Dakin Taro a Zariya

Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta yaba wa fitaccen mai taimakon al’umma, Malam Magaji Umar Dan Aljanna, bisa gina mata katafare...


Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta yaba wa fitaccen mai taimakon al’umma, Malam Magaji Umar Dan Aljanna, bisa gina mata katafaren dakin taro na zamani a Zariya.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya a Jihar Kaduna, DCF Aminu Amadu, ya bayyana hakan a yayin bikin sanya harsashin ginin dakin taron a Zariya.

DCF Aminu Amadu ya ce irin tallafin da Hukumar ke samu daga al’ummar Zariya, musamman daga Malam Magaji Dan Aljanna, ya taimaka wajen samun nasarar dakile gobara da sauran iftila’i.

Ya bayyana cewa ayyukan Hukumar sun taimaka wajen ceto rayuka da dukiyoyi da suka kai darajar sama da naira miliyan sittin.

Shugaban ya yi kira ga masu hannu da shuni da ’yan siyasa da su yi koyi da Malam Magaji Dan Aljanna wajen tallafa wa Hukumar domin ta samu damar sauke nauyin da ke kanta.

Da yake jawabi, Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Injiniya Jamilu Ahmad Muhammad, ya yaba wa Hukumar Kashe Gobara bisa yadda take gudanar da ayyukanta dare da rana domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce Karamar Hukumar Zariya da al’ummar yankin za su ci gaba da tallafa wa Hukumar da kayan aiki na zamani domin inganta ayyukanta.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, wanda Garkuwan Ayyukan Zazzau, Injiniya Balarabe Musa, ya wakilta, ya gode wa Malam Magaji Umar Dan Aljanna bisa wannan gagarumin aiki.

Ya bukaci masu hannu da shuni da sauran al’umma da su yi koyi da shi wajen tallafa wa hukumomin da ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Shi ma Malam Magaji Umar Dan Aljanna ya ce ya dauki nauyin gina katafaren dakin taron ne domin karfafa Hukumar da jami’anta tare da bayar da gudunmawarsa wajen inganta ayyukanta.

Ya ce muhimmancin aikin Hukumar wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma ya sa ya ga wajibi ne a tallafa mata domin ta kara inganta ayyukanta.

Dan Aljanna ya bukaci jami’an kashe gobara da su kara himma wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga gobara da sauran iftila’in da ka iya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da sauran al’umma da su ci gaba da tallafa wa Hukumar tare da ba ta cikakken goyon baya domin samun damar sauke nauyin da ke kanta.

No comments