A Duniyar sarauta, akwai shugabanni, akwai masu mulki, amma kaɗan ne ake samun waɗanda suka haɗa daraja, ilimi, hikima da kuma j...
A Duniyar sarauta, akwai shugabanni, akwai masu mulki, amma kaɗan ne ake samun waɗanda suka haɗa daraja, ilimi, hikima da kuma jin ƙai a zuciya. Daga cikin irin waɗannan fitattun shugabanni ne Mai Martaba Ambasada Malam Ahmed Nuhu Bamalli, Sarkin Zazzau, Sarkin da ke haskaka masarautar Zazzau da ɗaukaka ta musamman.
Shi jigo ne, ginshiƙi, kuma tauraron da ke haskaka sarautar Zazzau da darajar da ba ta misaltuwa. Tun kafin hawansa karagar mulki, ya riga ya kasance mutum mai cikakken tarihi na kima da daraja wanda ya ratsa duniyar diflomasiyya, ya wakilci ƙasa cikin ƙwarewa da mutunci, wanda hakan ya ƙara masa girma da hangen nesa irin na manyan shuwagabannin duniya.
Ba a nan kaɗai girman ya tsaya ba! Sarkin Zazzau, mutum ne mai zurfin ilimi, wanda Allah Ya azurta da basira da hikima. A fannin ilimin Addini shi kogi ne, a Boko kuwa nan ma ba a magana,hakan ya tabbatar da cewa shi Sarki ne da ke tafiya da zamani, amma duk da haka bai taɓa mantawa da asalin al’adar sa ba. Wannan haɗin gwiwa tsakanin ilimi da al’ada ya sa ya zama abin koyi ga masu sarauta da matasa baki ɗaya.
Idan aka zo ga halaye, to Sarkin Zazzau ya kasance abin misali na tawali’u da karamci. Duk da girman matsayinsa, yana saukowa zuwa ga talakawa, yana sauraron su, yana ba su kulawa da tausayi. Wannan hali nasa yasa jama’a suna ƙara kaunarsa, sun ɗauke shi bawai kawai a matsayin sarki ba, har ma a matsayin uba kuma jagora.
Bugu da kari,Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, na daga cikin Sarakunan Gargajiya na zamani da suka haɗa ilimi, ƙwarewa da kuma kyakkyawar manufa ta jagoranci. Rayuwarsa ta ƙunshi abubuwa masu yawa na alkhairi da ke bada mamaki, waɗanda suka bambanta shi da wasu Sarakuna a Najeriya.
Abu na farko da ya fi daukar hankali a rayuwarsa shi ne dogon tarihinsa a harkar diflomasiyya kafin hawansa karagar sarauta. Ya yi aiki a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Tarayyar Najeriya, inda ya wakilci ƙasar a matsayinsa na jakada a ƙasashe daban-daban, ciki har da Thailand. Wannan kwarewa ta duniya ta ba shi fahimta mai zurfi kan shugabanci, zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Wani abin alkhairi da ke bada mamaki game da Sarkin Zazzau shi ne matakin ilimi da ya kai. Ba sarki kawai ba ne, fasihi ne kuma haziki. Wannan ne yasa yake fahimtar kalubalen zamani, tare da neman mafita bisa ilimi da hikima, ba bisa al’ada kaɗai ba.
Haka kuma, Sarkin Zazzau ya shahara da sauƙin kai da kusanci da jama’a. Duk da matsayin da yake kai, yana mu’amala da talakawa cikin girmamawa, yana sauraron matsalolinsu kai tsaye. Wannan hali ya kara dankon zumunci tsakaninsa da al’ummar masarautar Zazzau dama jahar kaduna baki daya.
A fannin zaman lafiya, Sarkin Zazzau ya taka muhimmiyar rawa wajen kira da karfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin addinai da kabilu, musamman a Jihar Kaduna da ke fama da rikice-rikice lokaci zuwa lokaci. Yana amfani da murya da matsayinsa wajen jaddada muhimmancin fahimtar juna da zaman lafiya mai ɗorewa.
Bugu da ƙari, Sarkin ya nuna kulawa ta musamman wajen ci gaban matasa maza da mata. Yana ƙarfafa ilimi, koyon sana’o’i da tarbiyya, yana ganin su a matsayin ginshiƙan ci gaban al’umma,Wannan hangen nesa ya nuna yadda yake duba makomar masarautarsa da Najeriya gaba ɗaya.
Abin da ya kara bayyana alkhairinsa shi ne yadda yake haɗa al’adar gargajiya da shugabancin zamani. Yana mutunta al’adun Masarautar Zazzau, amma a lokaci guda yana maraba da sabbin dabaru da tunani da za su kawo ci gaba ba tare da lalata asali ba.
Sannan kuma, Sarkin Zazzau, Ambassador Alhaji Dr. Malam Ahmed Nuhu Bamalli, sarki ne da ke amfani da sarautarsa wajen gyara al’umma, karfafa zaman lafiya, ilimi da tarbiyya. Abubuwan alkhairi da ke rayuwarsa na ci gaba da zama abin koyi ga shugabanni da matasa, tare da tabbatar da cewa sarauta na iya zama hanyar hidimar jama’a da gina al’umma mai nagarta.
A cikin sarauta, akwai masu zama a kujera, akwai waɗanda suke cika kujerar da daraja. Hakika, Malam Ahmed Nuhu Bamalli yana daga cikin waɗanda suka ɗaukaka sarauta da martabarta. Yana tafiyar da mulki cikin hikima, yana kare al’ada, yana rungumar ci gaba.
A ƙarshe, za a iya cewa Sarkin Zazzau ba kawai sarki ba ne, gwarzon shugaba ne, wanda tarihinsa zai ci gaba da yaduwa da kuma haskakawa har zuwa ƙarni masu zuwa. Allah Ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana,Ya ƙarfafa masa iko, Ya kuma daɗa masa ɗaukaka da girma a idon duniya baki daya ameen ya Arrahman.
Muhammad Shafiu Ibrahim
Shafiun419@gmail.com

No comments