An bukaci Al’ummar Musulmi da su kara dagewa a cikin sauran kwanaki na watan Ramadan wajen yin addu’o’i da sauran ibadu, musamma...
An bukaci Al’ummar Musulmi da su kara dagewa a cikin sauran kwanaki na watan Ramadan wajen yin addu’o’i da sauran ibadu, musamman ta hanyar neman gafarta Allah domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Shugaban al’umma, Malam Bashir Umar Dattijo, ya yi wannan kiran a yayin da yake magana da ‘yan jarida a Zariya.
Malam Bashir Umar Dattijo ya bayyana cewa, kwanakin karshe na Ramadan na baiwa Musulmi dama ta musamman wajen kusantar Allah ta hanyar addu’a, tuba da sauran ayyukan ibada, musamman a wannan lokaci da kasa ke fuskantar matsalolin tsaro da Sauransu.
Ya yaba wa malaman bisa Dattako da sani ya kamata a yayin da sukee gudanar Tafsir na Ramadan a wannan shekara .
Shugaban al’umma, wanda Shi ne Dan Galadiman Madakin Zazzau ya shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da karfafa zumunci da zaman lafiya domin tabbatar da kwanciyar hankali a kasa.
Ya kuma bukaci matakan gwamnati uku da su samar da manufofi da shirye-shirye da zasu rage wahalhalun tattalin arziki da ‘yan kasa ke fuskanta, musamman matsalolin da suka biyo bayan tashin farashin man fetur.
Shugaban al’umma ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su tallafawa mabukata ta hanyar samar musu da abinci, tufafi da sauran muhimman kayan bukata domin su samu damar gudanar da bukukuwan Eid cikin mutunci.
Haka zalika, ya gargadi matasa da kada su yi amfani da miyagun kwayoyi da wasu muggan dabi’u a lokacin bukukuwan Eid da bayan haka.
Dan Galadiman Madakin Zazzau, Malam Bashir Umar Dattijo, ya shawarci al’umma da su yi amfani da darussa da koyarwar da suka samu a watan Ramadan tare da gyara halayensu domin su zamo mutane Nagari a Cikin al’umma

No comments