An bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da sauran kwanaki goma na watan Ramadan ta hanyar ƙara yin , addu’o’i da sauran ibadu...
An bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da sauran kwanaki goma na watan Ramadan ta hanyar ƙara yin , addu’o’i da sauran ibadu domin samun lada mai yawa daga Allahu SWt
Fitaccen malamin addinin Musulunci nan kuma mai taimakon jama’a a Zariya, Malam Magaji Umar Dan Aljanna, ne ya yi wannan kira a yayin da yake bayani kan muhimmancin kwanaki goma na ƙarshen watan Ramadan.
Malam Magaji Umar Dan Aljanna ya bayyana cewa kwanaki goma na ƙarshen watan Ramadan suna da matuƙar muhimmanci, a don haka ya kamata Musulmi su yi amfani da wadannan kwanakin yadda ya dace.
Ya kuma nuna cewa akwai darussa masu yawa da ke kunshe a cikin watan Ramadan waɗanda ya kamata Musulmi su riƙa kiyaye su a lokacin watan da ma bayansa.
Malamin addinin ya kuma buƙaci al’umma da kada su gajiya wajen yi wa ƙasa da shugabanninta addu’ar samun zaman lafiya da tsaro da kuma haɗin kai.
A cewarsa, zaman lafiya da haɗin kai da tsaro su ne ginshiƙan da ke kawo ci gaban ƙasa da bunƙasar tattalin arziki.
Kazalika Malam Magaji Umar Dan Aljanna ya shawarci matasa da su guji shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran munanan halaye da ka iya lalata makomarsu.
Ya ce neman ilimin addini da na zamani tare da koyon sana’o’i zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da kuma samun ci gaba mai ɗorewa.
Malamin addinin kuma mai taimakon jama’ar ya yi kira ga iyaye da su ƙara ƙaimi wajen tarbiyyar ‘ya’yansu yadda ya kamata domin sauke nauyin da ke kansu.

No comments