Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Makarantar Nurul Islam Academy ta Yaye Mahaddata Alƙur’ani 19 a Bikin Karo na Uku a Zariya

Makarantar Nurul Islam Academy for Arabic and Islamic Studies da ke Barakin Basawa Zariya ta gudanar da bikin yaye Dalibanta mah...

Makarantar Nurul Islam Academy for Arabic and Islamic Studies da ke Barakin Basawa Zariya ta gudanar da bikin yaye Dalibanta mahaddatan Alkur’ani da masu sauka su 18  karo na uku.

Da yake gabatar da nasiha, Daraktan Cibiyar Addinin Musulunci da Shari’a ta Jami’ar Ahmadu Bello Kongo, Dakta Sa’ad Abubakar ya ce dole mahaddacin Alkur’ani ya daidaita halayyarsa da koyarwar Alkur’ani da Sunnah. 

Ya kuma yaba da kokarin shugabannin makarantar wajen yaye mahaddata masu tarbiya da'a. 

A nashi jawabin, Malam Ahmad Garba Kaduna ya bayyana daukaka da falalar da Allah ke yi wa mahaddacin Alkur’ani mai girma.

A Jawabansu Babban Limamin Barakin Basawa Kaftin Muhammad Sani Usman da Shugaban makarantar Malam Abdullahi Sa’idu Basawa sun nuna farin cikinsu kan nasarorin da Suka samu.
Da yake Jawabi Babban Bako, kwamanda Barikin Basawa, Birgediya Janar Yakuba Wanda Kanal  Yusuf ya wakilce Shi ya taya daliban murnar kammala karatu tare da jan hankalinsu da su ci gaba da neman ilimi don ci gaban rayuwarsu.

Wasu Daga cikin daliban da aka yaye Abubakar Muhammad Sani da Khadija Muhammad Sani sun bayyana farin cikinsu tare da karanto wasu ayoyi daga Alkur’ani mai girma.

Bikin ya yaye daliban mahaddata Alkur'ani su 18  karo na uku, ya samu  halartar  Babban Limamin Depot Zariya da  Mataimakin Darakta sashen harkokin addini na IDIV Kaduna da Dakta Zakariya daga FUE Zariya da malamai da  iyaye da dimbin dalibai da sauransu.

No comments