Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Faith and Cultural Champions, Al'mannar Women Association ta shirya taron Fadakarwa ta Musamman ga Maza a Kan muhimmancin zuwa Awon ciki da haihuwa a Asibiti da Kula da lafiyar Jariri

Kwararriyar Likitan Yara da ke  Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Shika Zariya, Dr. Fatima Abdullahi, ta yi kira ga mata...



Kwararriyar Likitan Yara da ke  Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Shika Zariya, Dr. Fatima Abdullahi, ta yi kira ga mata masu juna biyu da su rika zuwa awon ciki da wuri domin tabbatar da lafiyar uwa da jariri.

Ta bayyana hakan ne a wajen taron Fadakarwa ga maza a Kan muhimmancin zuwa awon ciki da haihuwa a Asibiti da Kula da lafiyar Jariri, Wanda 
Faith and Cultural Champions, Al'mannar Women Association ta shirya Wanda ya gudana a Makarantar Firamare ta Sarkin Musa Kwarbai, Zariya.

Dakta  Fatima Abdullahi ta ce zuwa awon ciki  da wuri na bai wa ma’aikatan lafiya damar gano abubuwan da ka iya zama hadari ga rayuwa uwa da jariri.

Ta lissafo wasu alamomin hadari da suke samun mai juna biyu da suka hada da,ciwon kai, mai tsanani  da zazzabi mai zafi  da zubar jini, da yawan amai da  ciwon ciki , da sauransu.

Kwararriyar Likitan Yaran  ta bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne musamman ga maza da matasa da yara mata, tana mai jaddada cewa goyon bayan maza yana da matukar muhimmanci wajen ganin iyalansu masu juna biyu sun samu kulawar da ta dace.

Ta kuma roki sarakuna da  malamai, da shugabannin al’umma da su ci gaba da  irin wadannan shirye-shiryen goyon baya domin inganta lafiyar uwa da jariri a cikin al’umma.

A jawabinta, Shugaban kungiyar Matan Al’Manar, Hajiya Rabi Umar Sodangi, ta ce an shirya taron ne domin fadakar da maza da matasa kan muhimmancin zuwa awo, da  haihuwa a Asibiti tare kuma  da kula da lafiyar uwa da jariri.

Tun da farko a Jawabinta na maraba  , Hajiya Ummulkuthum Mohammed Ali, ta yaba wa mahalartan bisa jajircewar su wajen inganta kiwon lafiyar al’umma.

Da yake Jawabi wakilin Hakimin Zariya da kewaye, Mai Unguwan Madarkaci Alhaji Ibrahim Sarki, ya tabbatar da cewa sarakuna  za su ci gaba da tallafa wa kokarin kungiyar na wayar da kan magidanta kan muhimmancin barin Mata masu juna biyu suna zuwa awo da kuma haihuwa a asibiti.

Ya kuma yi alkawarin kara hadin gwiwa da hukumomin lafiya da kungiyoyin al’umma domin inganta dabi’un kula da lafiya a cikin iyalai.

Wasu daga cikin mahalarta sun bayyana cewa za su yada ilimin da suka samu ga sauran mutane domin amfanin mata masu juna biyu a Cikin al’umma.

Taken Taron: "Iyalina abun kulawata,  "Abun Alfahari na, ya samu halartar magidanta Maza da , matasa, da Shuwagabanin al'umma da Malaman addini da Shuwagabanin Mata daga sassa daban-daban na Zariya.


---

No comments