Kwararriyar Likitan Yara da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Shika Zariya, Dr. Fatima Abdullahi, ta yi kira ga mata...
Kwararriyar Likitan Yara da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Shika Zariya, Dr. Fatima Abdullahi, ta yi kira ga mata masu juna biyu su rika zuwa awo tun farkon daukar ciki domin tabbatar da lafiyar uwa da jariri, da kuma rage matsalolin da ka iya tasowa a cikin juna biyu.
Ta bayyana hakan ne a wajen taron wayar da kai a Kan muhimmancin Kula da Kiwon lafiyar Uwa Dana Jariri da Yara a Matakin Al’umma, wanda kungiyoyin Faith and Cultural Champions da Al’Mannar Women Association suka shirya, a Makarantar Firamare ta Sarki Musa, Kwarbai, Zariya.
Dr. Fatima Abdullahi ta ce zuwa awo da wuri na bai wa ma’aikatan lafiya damar gano abubuwan da ka iya zama hadari ga rayuwa uwa da jariri.
Ta lissafo wasu alamomin hadari a cikin juna biyu da suka hada da, mummunan ciwon kai, da zazzabi mai tsanani, da zubar jini, da yawan amaid da ciwon ciki , da sauransu.
Kwararriyar Likitan Yara. ta yi nuni da cewa taron ya mayar da hankali ne musamman ga mazaje, da matasa da ‘yan mata, tana mai jaddada cewa goyon bayan maza yana da matukar muhimmanci domin ganin matansu masu ciki sun samu kulawar lafiya yadda ta kamata.
Ta kuma roki sarakuna da malamai, da shugabannin al’umma da su ci gaba da tallafa wa irin wadannan shirye-shirye domin inganta lafiyar uwa da jariri a cikin al’umma.
A jawabin ta, Ameerah ta kungiyar Matan Al’Mannar, Hajiya Rabi Umar Sodangi, ta ce an shirya taron ne domin fadakar da maza da matasa kan muhimmancin zuwa awo, da haihuwa a Asibiti tare kuma da kula da lafiyar uwa da jariri.
Tun da farko a Jawabinta na maraba Ita , Hajiya Ummulkuthum Mohammed Ali, ta yaba wa mahalartan bisa jajircewar su wajen inganta kiwon lafiya a al’umma.
Da yake Jawabi wakilin Hakimin Zariya da kewaye, Mai Unguwan Madarkaci Alhaji Ibrahim Sarki, ya tabbatar da cewa sarakuna za su ci gaba da tallafa wa kokarin kungiyar na wayar da kan magidanta kan muhimmancin barin Mata masu juna biyu zuwa awo da kuma haihuwa a asibiti.
Ya kuma yi alkawarin kara hadin gwiwa da hukumomin lafiya da kungiyoyin al’umma domin inganta dabi’un kula da lafiya a cikin iyalai.
Wasu daga cikin mahalarta sun bayyana cewa za su yada ilimin da suka samu ga sauran mutane domin amfanin mata masu juna biyu a Cikin al’umma.
Taron ya samu halartar magidanta Maza da , matasa, da Shuwagabanin al'umma da Malaman addini da Jami'an kungiyar da kwararrun ma’aikatan kiwom lafiya daga sassa daban-daban na Zariya.
---

No comments