An bukaci mata masu juna biyu da su kara dagewa wajen zuwa cibiyoyin kiwon lafiya domin yin awo, don kare lafiyarsu da ta jarira...
An bukaci mata masu juna biyu da su kara dagewa wajen zuwa cibiyoyin kiwon lafiya domin yin awo, don kare lafiyarsu da ta jariransu.
Shugabar Kungiyar Matan Al-mannar, Hajiya Rabi Umar Sodangi, ta yi kiran ne a wajen taron wayar da kai kan muhimmancin yin awo da kungiyar tare da hadin gwiwar Faith and Cultural Champions suka shirya a Darur Sunnah, Kwarbai Zariya.
Hajiya Rabi ta ce manufar shirin ita ce ilimantar da mata kan yadda za su kula da lafiyar kansu da ta jarirai tun daga farkon ciki har zuwa haihuwa.
Ta bayyana cewa za su shafe watanni shida suna Shiga cikin al’umma, musamman Asibitoci da Masallatai da majalisi domin fadakar da matan aure da mazajensu kan muhimmancin fara zuwa awo da wuri.
Manajan Shirin, Haj. Rabi Sodangi ta roki samun goyon bayan hakimai, da masu unguwanni, da malamai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar shirin.
A nasa bangaren, jami’i a
Cibiyar Sadarwa da Tasirin Zamantakewa,. Muhammad Bello Murtala, ya ce bincike ya nuna cewa rashin zuwa awo na daga cikin manyan dalilan yawaitar mace-macen mata da jarirai, musamman a jihohin Kano da Kaduna.
Har ila yau, Tsohuwar jami’ar kiwon lafiya, Hajiya Safiya Ishak, wadda ta gabatar da lacca kan muhimmancin yin awo da haihuwa a asibiti, ta bayyana hadarin da mata ke fuskanta idan suka ki yin awo ko suka yi jinkirin zuwa asibiti lokacin nakuda.
Mai Unguwan Kwarbai A,Mal. Ibrahim Yahaya, da na Anguwar Alkali, Abdulhamid Muhammad, sun tabbatar da cikakken goyon bayan su domin cimma burin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.
Kazalika,Daya daga cikin mahalarta taron, Amina Adamu Abbas, ta bayyana jin dadinta da abubuwan da ta koya, wadanda za su taimaka mata wajen kula da lafiyarta da ta jaririnta.
Taron ya samu halartar sarakuna, da malamai da kungiyoyin mata da sauran masu ruwa da tsaki.

No comments