kimanin Daliban wata Makarantar Islamiya 200 ne Suka amfana da tallafin Kayan Makaranta na dubban Naira kyauta a Zariya. Da ...
kimanin Daliban wata Makarantar Islamiya 200 ne Suka amfana da tallafin Kayan Makaranta na dubban Naira kyauta a Zariya.
Da yake Jawabi a Yayin rabon kayan, Shugaban Gidauniyar, Alhaji Magaji Shitu, ya ce manufar tallafin ita ce a canza rayuwar yaran ta hanyar ba su ilimin addini da na zamani domin samu kyakkyawar rayuwa.
Ya Kara da cewa wannan ba shi ne na farko ba,KO a kwanakin baya, Gidauniyar ta dauki nauyin dinkawa s dalibai sama da dari na Makarantar Firameri Dahiru Kanti.
Alhaji Magaji Shitu ya jaddada bukata ga iyaye da su dage wajen tura 'ya’yansu makaranta a kan lokaci, tare da ba Gidauniyar goyon baya domin ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunkasa ilimi a yankin.
Ya kuma bukaci al’umma da su ba gwamnati cikakken goyon baya da hadin Kai don samu ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
A nashi jawabin, Mai Unguwan Rimin Danza, Alhaji Adamu Sharehu, ya yabawa Gidauniyar bisa gudummawar da take bayarwa ga ilimin yara, tare da kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyin masu Zaman kansu da su yi koyi da Gidauniyar Alh. Magaji Shitu Educational Foundation.
Kazalika, Mataimakin Shugaban Gidauniyar, Alhaji Umar Mai Jalingo, ya ce babban burin Gidauniyar shi ne ta tabbatar kowanne yaro ko yarinya ya sun samu ilimin addini da na zamani mai inganci don samun kykkyawar rayuwa.
Da take tsokaci Shugabar Makarantar Firameri Dahiru Kanti, Malama Rukkaya Ahmad, ta yaba da kokarin Gidauniyar tare da Kira ga iyaye da su kula sosai da halartar makarantar ‘ya’yansu da kuma karatunsu.
Wasu daga cikin daliban da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu da godiya bisa taimakon da suka samu Daga Gidauniyar.

No comments