W ani ɗan kasuwa daga Zariya mai suna Ahmed Muhammad Gusau ya shigar da ƙara a gaban kotu kan Sanata Abdu Kwari, Hajiya Amina Dalhatu Akilu,...
W
ani ɗan kasuwa daga Zariya mai suna Ahmed Muhammad Gusau ya shigar da ƙara a gaban kotu kan Sanata Abdu Kwari, Hajiya Amina Dalhatu Akilu, da Shehu Abdu Kwari, yana tuhumar su da aikata zamba da makirci a wata mu’amalar musayar fili da gida da ta janyo cece-kuce.
An shigar da ƙarar ne ta hannun Bashir Musa & Associates, inda aka bayyana cewa abin da waɗanda ake ƙara suka aikata na iya zama laifi a ƙarƙashin Sashe na 58 da 306 na Dokar Laifuka ta Jihar Kaduna ta 2017, waɗanda ke ɗauke da hukunci a ƙarƙashin Sashe na 59 da 307 na wannan doka.
Bisa ga takardun da aka gabatar a kotu, lamarin ya fara ne a kusa da watan Agusta 2025, lokacin da mai ƙara, Ahmed Muhammad Gusau, ya ga wani fili dake No. 5, Abubakar Mustapha Road, Kabama Layout, Sabon Gari, Zariya, wanda mallakin Sanata Abdu Kwari ne.
Gusau ya nuna sha’awa wajen samun filin, inda ya roƙi Shehu Abdu Kwari, ɗan uwan Sanata ɗin, da ya taimaka masa wajen sanar da shi da batun.
Shehu ya shaida masa cewa Sanata baya sayar da fili, sai dai yana yin musayar fili da wani fili.
Daga nan ne Gusau ya bayar da tayin musayar gidansa dake No. 17, Sale Annur Street, Kabama Layout, Sabon Gari, Zariya da filin Sanata dake Abubakar Mustapha Road.
Bangarorin biyu suka amince cewa Sanata zai karɓi gidan Gusau mai Certificate of Occupancy No. 03311-10d51-n2732-10d51-n2337-r943, wanda aka kiyasta da kimar naira miliyan 60, yayin da Gusau zai karɓi filin Sanata wanda aka kiyasta da naira miliyan 20.
Kodayake gidan ya fi fili tsada, Gusau ya amince saboda yana son wurin sosai kuma yana da niyyar fara gini nan da nan.
Bayan amincewa, an ce Sanata Kwari ya bukaci a rubuta Deed of Assignment ɗin da sunan matarsa Hajiya Amina Dalhatu Akilu, saboda takardar mallaka ta fili tana da sunanta.
Mai ƙara ya amince, lauya ya shirya takardun, sannan aka sanya hannu a gaban Sanata, Shehu Abdu Kwari, Abdurrazaq Abdu Kwari (wanda ake kira Babangida), da Mai unguwa, wanda ya shaida komai.
Bayan ɗan lokaci, Shehu ya sanar da mai ƙara cewa akwai saura ₦30,000,000, amma Sanata ba zai iya biya a lokacin ba saboda ɗansa zai yi aure.
Gusau ya amsa da cewa bai damu da hakan ba, abin da yake so kawai shi ne ya fara gina gidan, kuma Sanata ya amince.
Bayan haka, Gusau ya tura ma’aikatansa zuwa wurin don fara gini. Ya sayi dukkan tubalin daga kamfanin Sanata mai suna A.A. Kwari Blocks dake kan titin Samaru, Zariya.
Da ginin ya kai matakin rufin bene, wasu jami’an KASUPDA suka bayyana daga babu inda suka dakatar da aikin, suna cewa Sanata Abdu Kwari ne ya umurce su da hakan.
A lokacin, an ce Gusau ya riga ya kashe fiye da ₦27,600,000 a aikin ginin, ban da kudin filin da kansa.
Bayan haka ne, wadanda ake ƙara suka canza maganarsu, suka ce fili nasu ne, kuma mai ƙara bai da hakkin gina a kai ba.
Mai ƙara ya ce an yi masa zamba domin sun jawo shi ya gina gida a kan filin nasu, sannan daga baya suka musanta yarjejeniyar bayan ya kashe kuɗi masu yawa da lokaci.
Takardar karar ta ce idan aka tabbatar da waɗannan abubuwa, hakan na nufin laifin haɗin baki (conspiracy) da yaudara (cheating) ne, wanda ya sabawa Sashe na 58 da 306, kuma yana ɗauke da hukunci a ƙarƙashin Sashe na 59 da 307 na Dokar Laifuka ta Jihar Kaduna ta 2017.
Lauyoyin mai ƙara — Bashir Musa, S.S. Yusuf, da M.A. Babaji — sun roƙi kotu da ta gurfanar da waɗanda ake ƙara tare da ɗaukar matakin hukunci idan aka tabbatar da laifin su.
Kotu ta sanya ranar 27 ga watan Nuwamba, 2025 domin fara sauraron shari’ar, wadda ke ɗauke da zarge-zargen zamba, karya yarjejeniya da haɗin baki.


No comments