Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Ku ƙara ba ni dama domin kammala gyaran Najeriya da na fara - Tinubu

By Sani mustapha  Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi ’yan Najeriya su kara ba gwamnatinsa dama domin ta kammala tsare-tsa...

By Sani mustapha 




Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi ’yan Najeriya su kara ba gwamnatinsa dama domin ta kammala tsare-tsare da sauye-sauyen da ta fara.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata addu’ar Juma’a ta musamman a Masallacin Kasa da ke Abuja, a wani bangare na shirye-shiryen bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, wanda ya wakilci Tinubu a wajen taron, ya ce gwamnati na kokarin gyara kura-kurai da damar da gwamnatocin baya suka rasa.

Ya bukaci ’yan Najeriya kada su yanke kauna, yana mai cewa zaman lafiya da ci gaba za su dawo yayin da ake ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

Tinubu ya ce Najeriya na kan turbar da ta dace, kuma ya yi kira ga al’umma su ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa domin ta kammala ayyukan da ta fara.

No comments