Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta sauya fasalin bangaren ilimi a fadin Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na 2025 na Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Barewa,,Wanda ya gudana...



Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na 2025 na Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Barewa,,Wanda ya gudanar a zauren taro na  Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar da ke Zariya.

Gwamnan Wanda Kwamishinan Ilimi na jihar, Farfesa Sani Sambo, ya wakilta  ya ce an ware kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin jihar ga ilimi a cikin kasafin kudi na Shekara uku da suka gabata tare da cigaba da gyaran makarantu da inganta kayan koyo da koyarwa a fadin jihar.

Ya Kuma bayyana cewa kimanin yara 300,000 da ba sa zuwa makaranta aka mayar da su Makarantar cikin tsarin ilimi na bai-daya, a yayin da Kuma ake ci gaba da kokarin shigar da tsarin ilimin Almajirai cikin tsarin ilimi na yau da kullum.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta tattauna da kungiyoyin kwadago na sauran Manyan Makarantu  mallakin jihar, biyo bayan warware rikicin kungiyar Malamai ta Jami’ar Jihar Kaduna. 

Ya ce an kafa kwamitin mutum 9 domin tattauna batutuwan da suka rage da suka shafi Manyan Makarantun.

Tun da farko da yake jawabi , Shugaban taron kuma tsohon Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon, wanda Alhaji Muhammad Ibrahim Turakin Guru ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wata dama ta sake haduwa da tsoffin abokan kanaratu  da sauran fitattun Daliban Kwalejin.

Janar Gowon ya tuna da dadaddiyar  alakarsa da Kwalejin Barewa, yana mai bayyana farin cikinsa kan irin nasarorin da tsofaffin daliban makarantar suka samu.

Ya Kara da cewa  Kwalejin Barewa ta samar da fitattun ’yan Najeriya da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa.

Tsohon Shugaban Kasar har ila yau ya jaddada cewa dabi’un ladabi, kwazo da kishin da suka koya a Kwalejin Barewa har yanzu suna ci gaba da tasiri a rayuwarsu. 

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Tsofaffin ÆŠaliban Kwalejin Barewa, Janar Alwali Kazir mai ritaya, ya yi kira da a Kara karfafa hadin gwiwa da  rikon amana tare da Samar da  ingantaccen shugabanci domin tabbatar da cewa an mayar da kungiyar  mai hangen nesa da za ta iya bayar da gudummawa ga ci gaban kasa.

Ya ce taron shekara-shekara na BOBA wata muhimmiyar dama ce ta gabatar da rahoton ayyukan kungiyar, duba halin da take ciki ta fuskar kudi da gudanarwa, tantance nasarorin da aka samu da kuma tsara hanyar da za a bi a nan gaba.

Janar Kazir ya yi nuni da cewa shugabancin kungiyar ya samu ci gaba wajen inganta sadarwa tsakanin Manyan Tsofaffin ÆŠaliban da kanana da Kuma rassar kungiyar na jihohi, ta hanyar karfafa tsarin gudanarwa tare da samar da damar shiga harkokin kungiyar ga kowa.

Ya kuma bayyana cewa shirye-shirye na gudana domin gudanar da lacca da bikin bayar da lambobin yabo na kungiyar, wanda ake sa ran gudanar da shi a watan Nuwamba na wannan shekara

Har ila yau, Shugaban Kungiyar Tsofaffin ÆŠaliban ya bukaci Tsofaffin ÆŠaliban da su ba da Gudunmuwa sosai wajen  ci gaban kungiyar da taimakawa Kwalejin da Kuma inganta Jin dadi da Walwalar 'ya'yan kungiyar. BOBA 

Taron kungiyar Tsofaffin ÆŠaliban Kwalejin Barewa na 2025, ya samu halartar wakilan Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da Sarkin Yawuri, da sauran fitattun ’ Tsofaffin Daliban Kwalejin Barewa da Sauransu.

No comments