Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Fityanul Islam Zaria Ta Nuna Damuwa Kan Kama Sheikh Sani Khalifa, Ta Buƙaci Gaggawar Sakin Sa

Daga Usman Abubakar Kusfa Ƙungiyar Fityanul Islam ta Ƙasa, reshen Karamar Hukumar Zaria, ta bayyana bacin ranta da takaicinta ka...


Daga Usman Abubakar Kusfa
Ƙungiyar Fityanul Islam ta Ƙasa, reshen Karamar Hukumar Zaria, ta bayyana bacin ranta da takaicinta kan kama Sheikh Sani Khalifa da jami’an tsaro suka yi tare da tsare shi na wani lokaci.

A cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Zaria ƙarƙashin jagorancin Abdulra’uf Shehun Tasi’u (Kusfa), lamarin ya jefa iyalai, almajirai, al’ummar gari, masoya da kuma ƙungiyoyin addini cikin damuwa da tashin hankali.

Ƙungiyar ta yi kira ga dukkan mahukuntan da abin ya shafa da su gaggauta sakin Sheikh Sani Khalifa, tana mai jaddada cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma. Ta ce kamar yadda wasu manyan shugabanni suka bayyana, sakin malamin zai zama alheri ga kowa da kowa, musamman ganin irin muhimmancin addu’a da zaman lafiya ga cigaban ƙasa.

Fityanul Islam ta kuma yaba da ƙoƙarin Shugaban Karamar Hukumar Zaria, tare da miƙa godiya ta musamman ga Uba Sani, Gwamnan Jihar Kaduna, bisa rawar da yake takawa wajen ganin an samu mafita cikin salama.

Haka kuma, ƙungiyar ta nuna godiya ga Abbas Tajuddeen, bisa kulawa da nuna damuwa kan lamarin, tana mai cewa irin wannan mataki na jagoranci na taimakawa wajen kwantar da hankulan al’umma.

Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan kira na samun goyon bayan Shugaban Fityanul Islam na Jihar Kaduna da na Ƙasa, Sheikh Arabi, tare da goyon bayan masoya darikun sufaye da al’ummar Musulmi baki ɗaya.

A ƙarshe, Fityanul Islam ta roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya fitar da Sheikh Sani Khalifa lafiya, Ya tabbatar da gaskiya, tare da kawo ƙarshen lamarin cikin salama.

No comments