Kakakin Majalisar Tarayya Abbass Tajuddeen ya mana Laifin da wajibi mu nesanta Tsangayarmu da sake kokarin mara masa Baya. Domin...
Amma tunda ya zama Speaker Ba a taba mana godiya ba,ba a taba baiwa Tsangayarmu ko kwayar Shinkafa ba,hakazalika duk ababen Alherin da ake Rabawa ba a taba Bamu ba,ba a saka mana Solar a Makarantunmu ba,ba a taba baiwa Tsangayarmu Mashin ko Kayan abincin da ake Rabawa ba,duk da Tarin Mabiyan da Tsangayar Young Shiekh ke dasu. Amma muna Gani an Janyo duk malaman da suka Yaki Kakakin Majalisar ana musu Alheri,wasu ma an karramasu.
Don haka zamu Umarci Mabiyanmu su yi Abunda ya Dace,ba zamu Tursasasu su zabi Tajuddeen Abbass ba,amma idan suna da Ra'ayin Zabensa ba zamu hanasu ba,amma mu ba zamuyi kiran a zabeshi ko kar a zabeshi ba.
Daga
Tsangayar Young Shiekh Zaria.

No comments