Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa, Zaria, ta yi ƙaramin hukunci a shari’ar batanci da ke tsakanin Sarkin Zazzau...
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa, Zaria, ta yi ƙaramin hukunci a shari’ar batanci da ke tsakanin Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, da tsohon Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, inda ta hana mai ƙara damar yin jawabi saboda rashin bin umarnin kotu.
A zaman da aka ci gaba da shi a ranar Laraba, Mai Shari’a Yakubu Badamasi ya bayyana cewa ba za a bai wa mai ƙara damar yin magana ba, saboda ya gaza bin umarnin kotu da aka riga aka bayar.
Kotun ta riga ta ci tarar naira dubu dari biyu (₦200,000) ga mai ƙarar saboda rashin nuna ƙwarewa wajen shigar da ƙarar, tare da la’akari da wahalar da lauyoyin ɓangaren da ake ƙara suka sha wajen zuwa kotu daga Lagos, Abuja da Kaduna.
Duk da wannan umarni, mai ƙarar bai biya tarar ba, wanda ya sa kotu ta jingina da ƙa’idar doka da ke cewa wanda ya saɓa wa umarnin kotu ba za a saurare shi ba har sai ya gyara laifinsa.
Saboda haka, kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga Yuni, 2026, domin a cika sharadin bin umarnin kotu.
A wani lamari mai alaƙa da wannan, wata shari’a da Dr. Nasiru Bashari Aminu ya shigar kan Sarkin ma ta fuskanci tangarda ta fuskar bin ka’idojin kotu.
A yayin shari’ar, lauyoyin mai ƙara sun gano cewa lauyan mai ƙara ya gabatar da takardar Pre-Trial Conference Sheet ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya saɓa da tsarin kotu.
Lauyoyin sun bayyana cewa Form 16 (Sanarwar Pre-Trial Conference) dole ne rajistara na kotu ya fitar tare da haɗa shi da Form 17, amma ba a bi wannan tsari ba a wannan shari’ar.
Lauyoyin Sarkin Zazzau, ƙarƙashin jagorancin Barrister Morris Odey tare da A. U. Bamalli da M. K. Jonathan, sun ƙalubalanci wannan kuskure, suna mai cewa babban saɓa doka ne.
Mai Shari’a Badamasi ya ɗage wannan ɓangare na shari’ar zuwa ranar 16 ga Yuni, 2026, domin yanke hukunci.
An shigar da ƙarar ne daga Dr. Nasiru Bashari Aminu, wanda ke ƙalubalantar Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, kan zargin ɓata sunan mahaifinsa a wata hira da ya yi da Radio France Internationale (RFI).
A cikin hirar, Sarkin ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin zaɓen sarautar Zazzau kafin ya samu nasarar zama sarki.
A baya, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kaduna ta riga ta yi watsi da wata ƙara da ke neman tsige Sarkin a ranar 19 ga Maris, 2025.
Rikicin ya samo asali ne lokacin da tsohon Wazirin Zazzau kuma ɗaya daga cikin masu zaɓen sarki, Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu, ya ƙalubalanci nadin Sarkin da gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta yi a Oktoba 2020.
Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa ƙarar ta wuce lokacin da doka ta tanada (statute-barred), don haka ba za a saurare ta ba, tare da yin watsi da duk wani hujja na neman ƙarin lokaci.

No comments