Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Sarkin Zazzau Ya Shawarci Sabon Darakta-Janar na NIPHID Kan Ƙwarewa da Ci Gaba

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya shawarci sabon Babban  Daraktan  Cibiyar Kula da Lafiyar Al’umma da C...

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya shawarci sabon Babban  Daraktan  Cibiyar Kula da Lafiyar Al’umma da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa, da ya Sanya   ƙwarewa da  riƙon amana da jajircewa wajen gudanar da ayyukansa domin bunƙasa da ci gaban cibiyar.

Ya ba da wannan shawara ce a lokacin da Sabon Babban Daraktan ya jagoranci manyan jami’an cibiyar suka kai masa ziyarar ban  girma a fadarsa da ke Zariya.
Wakilinmu Ibrahim Suleiman na da cikakken rahoton 
.

Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya jaddada buƙatar da Ake da ita ga Sabon Babban Darakta da ya yi aiki tuƙuru domin samun gagarumin ci gaba mai ma’ana Kasancewar Shi ne Shugaba na Farko da zai Jagoranci Cibiyar bayan an Daga darajar ta

Ya kuma bayyana cewa tafiya da kowa ba tare da nuna bambanci ko wariya ba, zai ƙara dankon zumunci da  haɗin kai, nasara da dorewar ci gaba.

Mai martaba Sarkin har ila yau ya  buƙaci sabon Shugaban da ya ba da fifiko wajen Bai wa ma'akatansa  horo a Kai akain domin ƙara ƙwarewa da inganta nagartar aiki.

Sannan ya yi kira ga ma’aikatan  da su bai wa sabon Shugaban cikakken goyon baya da haɗin kai da shawarwari masu amfani domin ɗaukaka martabar cibiyar a cikin Nijeriya da ma ƙasashen waje.

Tun da farko a jawabinsa, Sabon Shugaban Cibiyar , Dakta Abdullahi Aminu Dalhatu, ya ce sun zo fadar Mai martaba Sarkin ne  domin neman albarka da shawarwarin  daga Mai Martaba Sarkin. a matsayinsa na uba.

Ya yi nuni da cewa tun bayan kama aikinsa  watanni uku da suka gabata, ya gudanar da aikin tantance ma’aikata domin sanin ainihin adadin waɗanda ke halartar aiki da kuma waɗanda ba sa zuwa aiki.

Dakta Dalhatu ya kuma nemi samun goyon baya da haɗin kan Masarautar Zazzau wajen ciyar da cibiyar gaba.

Sabon Babban Darakta Cibiyar Kula da lafiyar Al'umma da cututtuka masu yaduwa ta kasa, Dakta Abdullahi Aminu Dalhatu  ya samu rakiyar manyan jami’an gudanarwar cibiyar.

No comments