Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Kira ga Shugabanni su Yi Koyi da Salon Mulkin Sardaunan Sokoto

An yi kira ga masu riƙe da muƙaman gwamnati da su yi koyi da salon mulkin marigayi Firaministan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardaun...


An yi kira ga masu riƙe da muƙaman gwamnati da su yi koyi da salon mulkin marigayi Firaministan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, musamman a fannoni na rikon gaskiya da amana, kishin ƙasa da kuma jajircewa wajen ciyar da al’umma gaba.
 Sananan malamin addinin Musuluncin nan kuma kuma Mai taimako al’umma a Zariya, Malam Magaji Umar Dan Aljanna, yayin da yake zantawa da manema labarai dangane da cikar marigayi Sardaunan Sokoto shekaru sittin da rasuwa
 Ya kuma  bayyana cewa shugabannin da suka gabata sun gudanar da mulkinsu bisa gaskiya da adalci, ba tare da nuna9 bambanci na addini ko ƙabila ba, inda ya ce wannan ne ya taimaka wajen gina tubalin zaman lafiya da ci gaban Arewa a wancan lokaci.
Dan Aljanna ya jaddada cewa ya dace shugabannin da ke kan madafun iko a yanzu su waiwayi tarihi tare da yin koyi da irin kyakkyawan shugabancin marigayi Sardaunan Sokoto, ta hanyar aiwatar da ayyukan alheri da za a rika tunawa da su ko bayan sun bar mulki.
Kun
A wani bangare kuma  Malam Magaji Umar Dan Aljanna ya buƙaci gwamnonin jihohin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki a yankin da su duba halin da Gidan Rediyon Najeriya Kaduna ke ciki, tare da kawo masa ɗaukin gaggawa domin dawo da martaba da darajar da aka san shi da ita.

Ya bayyana cewa Gidan Rediyon Najeriya Kaduna na daga cikin muhimman cibiyoyin da marigayi Sir Ahmadu Bello ya assasa a lokacin rayuwarsa, yana mai nuna damuwa cewa a halin yanzu gidan rediyon na fuskantar matsaloli masu yawa da ke buƙatar tallafi domin hana shi durƙushewa.

Har ila yau, malamin ya yi kira ga al’ummar ƙasa da su ƙara himma wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya, tsaro da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
Ya kuma ja hankalin iyaye da su ƙara sanya ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu, musamman duba da yadda ake fuskantar tabarbarewar ɗabi’a a tsakanin matasa a wannan zamani.
Malam Magaji Umar Dan Aljanna ya kuma shawarci matasa da su rungumi neman ilimin addini da na zamani, tare da koyon sana’o’in hannu domin samun dogaro da kai.
Kazalika, ya buƙaci al’umma da su sanya tsoron Allah a cikin dukkan al’amuransu na yau da kullum, tare da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya da haɗin kai ta hanyar samar musu da muhimman bayanai da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro da ke addabar yankin Arewa da ƙasar baki ɗaya.
LolMalam Magaji Umar Dan Aljanna ya yi kira ga matakan gwamnati da su fito da tsare-tsare masu inganci da za su taimaka wajen inganta rayuwar talakawan Najeriya.

No comments