Kungiyar Dattawan lardin Zazzau, karkashin jagorancin Galadiman Raya Kasar Zazzau, Alhaji Sabo Tukur, ta kai ziyarar jaje ga Dan...
Kungiyar Dattawan lardin Zazzau, karkashin jagorancin Galadiman Raya Kasar Zazzau, Alhaji Sabo Tukur, ta kai ziyarar jaje ga Dan Buran Zazzau, Barden Keffi, Alhaji Sani Mahmud Sha'aban, bisa jarabawar da ta sa meshi na rushe masa katafaren gidansa da cibiyoyin sana'o'in da ya gina domin amfanin al'ummar Zazzau da Jihar Kaduna baki daya.
Shugaban kungiyar, Galadiman Raya Kasar Zazzau, Alhaji Sabo Tukur, ya bayyana cewa sun zo ne domin jajanta masa bisa wannan lamari na rashin dadi da ya faru da shi. Ya kuma roke shi da ya kara hakuri tare da addu'ar Allah ya ba shi mafita.
A jawabansu daban-daban, mambobin kungiyar sun roki Allah Madaukakin Sarki ya ba Alhaji Sani Mahmud Sha'aban juriya da ikon cin wannan jarabawa.
Sun bayyana shi a matsayin mutum mai taimakon jama'a kuma mai kishin ci gaban al'umma, tare da Karfafa masa Gwiwar cewa Allah ya bashi mafita nan da ba jimawa ba.
Da yake mayar da jawabi, Dan Buran Zazzau, Barden Keffi, Hon. Sani Mahmud Sha'aban, ya gode musu bisa wannan ziyara, inda ya bayyana ta a matsayin cikakkiyar alamar kauna da soyayya.
Hon. Sani Mahmud Sha'aban ya yi kira ga Dattawan da su yi iya kokarinsu wajen wayar da kan jama'a game da halin da ake ciki, tare da rokon su da su tsaya tsayin daka wajen sauke nauyin da ke kansu a matsayinsu na Dattawa.
Dan Buran Zazzau ya sake godiya a gare su bisa ziyarar tare da ba su tabbacin samun cikakken goyon bayansa domin cimma nasara.
Sannan ya ba su tabbacin cewa wannan abun da ya faru da Shi ya dauke Shi matsayin Jarabawa Daga Allahu (SWt), Amma ya ce wannan ba zai sa Shi ya ja da baya ba a Kan Kishin lardin Zazzau

No comments